Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude baje kolin hanyoyin samar da kayayyakin kasa da kasa karo na farko CISCE, da dandalin bunkasa kirkire-kirkiren hanyoyin samar da kayayyaki a nan birnin Beijing, a yau 28 ga watan Nuwamba, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. Ya ce, kiyaye ingancin hanyoyin samar da kayayyaki ga masana’antun duniya, wani muhimmin tabbaci ne na bunkasa tattalin arzikin duniya.
Kasar Sin ta shirya baje kolin ne don samar da dandalin ga kasashen duniya, da zummar sa kaimi ga zurfafa hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare tsakanin dukkan bangarori.
Ya ba da shawarar zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin masana’antu da hanyoyin samar da kayayyaki, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki tare don tabbatar da tsaro, da kwanciyar hankali, da daidaito, da gaskiya, da hada kai, da moriyar juna a fannin hanyoyin samar da kayayyaki ga masana’antu. (Mai fassara: Yahaya)