Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta dage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), zuwa watan Janairun 2024.
Hakan zai sa ya ci gaba da zama a gidan yari har sai ya cika ka’idar belinsa ta kudi Naira miliyan 300.
- Rikicin Shugabanci: PTD Ta Ce Kwamared Egbon Kawai Ta Sani A Kaduna
- Fintiri Ya Sanar Da Tallafin Dubu 10 Ga ‘Yan Bautar Ƙasa A Adamawa
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce, ta gurfanar da Emefiele bisa zarginsa da laifuka shida, ciki har da zargin badakalar kudi Naira biliyan 1.6 da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.
Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin sake zama kan shari’ar.
Shugaba Bola Tinubu ne, ya dakatar da Emefiele daga mukaminsa a ranar 9 ga watan Yuli 2023, don gudanar da bincike kan yadda ya tafiyar da ayyukan ofishinsa.