• English
  • Business News
Wednesday, August 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fito Da Manhajar DSO Na Aikin Talbijin Kwanan Nan – Minista

by Sulaiman
2 years ago
in Labarai
0
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fito Da Manhajar DSO Na Aikin Talbijin Kwanan Nan – Minista
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta na nan ta na aiki tuƙuru domin fito da sabuwar manhajar da za a yi amfani da ita wajen aikin talbijin a duk faɗin ƙasar nan, wato ‘Digital Switch Over’ (DSO).

Hadimin musamman kan harkar yaɗa labarai na ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya bayyana a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar cewa, ministan ya faɗi haka ne a Abuja a ranar Litinin a lokacin da ya ke buɗe babban taron sanin makamar aiki na shugabannin gudanarwa na Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA).

  • An Sake Mayar Da Emefiele Gidan Yari Saboda Gaza Cika Sharudan Beli
  • Rikicin Shugabanci: PTD Ta Ce Kwamared Egbon Kawai Ta Sani A Kaduna

Ya ce: “Ina kuma so in yi amfani da wannan damar in nanata sadaukarwar Gwamnatin Tarayya ga tsarin ‘Digital Switch Over’, domin kuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta na ta aiki tuƙuru kan manhajar DSO wadda ba za ta gaza ba; wadda za a yi amfani da ita a birane da ƙauyukan Nijeriya. Ana sa ran cewa hukumar NTA, a matsayin ta na babbar mai ruwa da tsaki a tsarin na DSO, za ta taka muhimmiyar rawa a ciki.”

Don haka Idris ya ƙalubalanci NTA da ta yi zuzzurfan tunani kan yadda yanayin aikin jarida ya ke sauyawa, musamman da yake sababbin fasahohin zamani na shigowa kuma zaɓin masu kallo shi ma ya na canzawa tare da kawo ƙalubale da kuma damarmaki.

Ya ce: “Sadaukarwar mu ga tabbatar da inganci da kuma karɓar sauyi shi ne gaba da komai. Tilas ne NTA ta ci gaba da rungumar canji, ta na karɓar sababbin dabaru a yayin da ta ke riƙe da darajar aikin jarida mafi girma sau da ƙafa.

Labarai Masu Nasaba

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

“Wannan taron ya zo ne a daidai lokacin da masu kallo su ke ta samun zaɓi daban-daban na inda za su samu bayanai, musamman ma da yake yanzu soshiyal midiya na da ƙarfi tare da tasiri wajen yaɗa labaran ƙarya da yaudara da ke akwai a cikin ta; don haka muhimmancin taro irin wannan ba ƙarami ba ne.”

Ya lura da cewa ɗaga ƙarfin hotuna da sautin da aka samu a NTA daga matakin ‘standard definition’ (SD) zuwa matakin ‘high definition’ (HD) ya na yin tasiri matuƙa a wajen jama’a masu kallo, ya ƙara da cewa tilas ne a samar da wannan tsarin a dukkan tashoshin NTA da ke faɗin ƙasar nan idan ana so a cimma manufar da ake buƙata.

Dangane da batun Tsarin Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) na gwamnatin Shugaba Tinubu kuwa, wanda ya bayyana da cewa ba a taɓa samun dabarar gina ƙasa ta ɓangaren zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya kamar ta ba, don haka a cewar Idris, “haƙƙi ya rataya a wuyan NTA ta ci gaba da wayar da kan ‘yan Nijeriya kan nasarorin da ake samu a dukkan ɓangarori, kuma ta tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun fahimci alƙiblar da gwamnatin Tinubu ta fuskanta wajen yaɗa labarai da tsara shirye-shiryen talbijin.

Ministan ya buƙaci NTA da ta dage wajen dawo da martabar da aka san ta da ita a baya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Hukumomin TsaroMinistan Yaɗa Labarai
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Gudanar Da Dandalin Sada Zumunta Na Basi Na Shekarar 2023

Next Post

Sojoji Sun Gargadi Masu Zanga-Zanga A Nasarawa

Related

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar
Manyan Labarai

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

17 minutes ago
Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Labarai

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

8 hours ago
Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025
Labarai

Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

9 hours ago
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin
Labarai

Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna

10 hours ago
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

12 hours ago
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin
Manyan Labarai

Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

14 hours ago
Next Post
Sojoji Sun Gargadi Masu Zanga-Zanga A Nasarawa

Sojoji Sun Gargadi Masu Zanga-Zanga A Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

August 27, 2025
Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

August 26, 2025
Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

August 26, 2025
Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

August 26, 2025
Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

August 26, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna

August 26, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

August 26, 2025
Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

August 26, 2025
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 26, 2025
Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

August 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.