Yanzu haka kasashe da ragowar bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, na shirin hallara a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, don gudanar da taro kan sauyin yanayi ko COP28, inda ake sa ran shugabannin kasashen duniya za su tattauna kan matsalolin dake hana ruwa gudu game da magance matsalar sauyin yanayi dake ci gaba da addabar sassan duniya ta fannoni daban-daban.
A taron da ya gudana a kasar Masar a bara, galibin shugabannin kasashen da suka gabatar da jawabai a taron, sun kara yin kira ne ga kasashe masu karfin tattalin arziki, da su dauki matakai na zahiri maimakon maganar fatar baki da suka saba yi a duk lokacin da aka kira irin wannan taro ko wani dandali mai kama da wannan, domin shawo kan illolin da sauyin yanayin ke haifarwa, kamar zafi da fari da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa dake tafe da mamakon ruwan sama da makamantansu.
Haka kuma sun yi kashedin cewa, lokaci fa yana kurewa, kuma duk wani jan kafa kan wannan batu, babu abin da zai haifar illa haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
- An Kammala Aikin Bututun Karkashin Ruwa Na Sabuwar Hanyar Sin Da Ta Ratsa Teku
- Sin Na Ba Da Gudummawa Wajen Samar Da Abinci Da Tsarin Samar Da Kaya A Duniya
Wani rahoto da hukumar kula da makamashi ta MDD ta fitar na nuna cewa, a shekaru 8 dake tafe, ana iya cewa, duniya ta kama hanyar fuskantar zafi mafi tsanani a tarihi. Shin ina muka dosa? Hukumomin MDD gami da kungiyoyi masu zaman kansu ma, sun yi gargadin cewa, an samu karuwar matsalar karancin abinci mai gina jiki a cikin shirye-shiryen kula da abinci mai gina jiki a fadin yankin kahon Afirka, wannan ma wata alama ce ta matsalar sauyin yanayi, haka kuma mutane da dama sun rasa abubuwan rayuwa, da hanyoyin da za su iya magance wannan bala’i, sannan kuma sun dogara baki daya kan taimako don biyan bukatunsu na yau da kullum, matakin da zai iya kalubalantar farfadowar fari.
A yayin da ake shirin gudanar da taron COP28, wanda ke nufin zama karo na 28 na babban taron kasashen duniya kan tsarin sauyin yanayi na MDD a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya jaddada cewa, akwai bukatar shugabannin kasashen duniya da za su halarci taron na wannan mako, da su dakile ci gaban mummunan dumamar yanayi da ake fuskanta, kafin a shiga wani mummunan yanayi.
Kalamansa na zuwa ne, bayan da a karshen mako ya ganewa idonsa yadda curin dutsen kankara ke saurin narkewa a Antatika, saurin da ya ninka sau uku fiye da yadda ake gani a farkon shekarun 1990.
Masana na cewa, yanzu haka, mummunan yanayi na zafi na karuwa fiye da kima, yayin da kankara ke raguwa ga kuma yanayi mai tsanani, kuma kowa ya san mafita. Tilas ne shugabanni su dauki mataki don takaita karuwar yanayin zafin duniya zuwa ma’aunin digirin Celcius 1.5, da kare mutane daga matsalar yanayi, da kawo karshen amfani da makamashin dangin kwal, mai da iskar gas dake gurbata muhalli.
Yanzu dai dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Ko dai duniya ta mayar da hankali wajen daukar managartan matakan magance wannan matsala ko kuma duniya ta ci gaba da shiga hali na kunci sakamakon matsalar sauyin yanayi. (Ibrahim Yaya)