A jiya ne aka kammala aikin gina babban bututun karkashin ruwa na sabuwar hanyar da ta ratsa teku ta kasar Sin a lardin Guangdong da ke yankin kudancin kasar Sin.
Bututun, wanda ya kai tsawon kimanin kilomita 6.8, wani bangare ne na wata babbar hanya mai tsawon kilomita 24 da ta hada Shenzhen da Zhongshan, da kowane ke gefen gabar kogin Pearl.
- Za Mu Gudanar Da Bincike Kan Kundin Takardun Shari’ar Zaben Gwamnan Kano – NJC
- Fasahar 5G A Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Mai Dorewa
Hanyar da ta hade Shenzhen da Zhongshan, wani muhimmin aikin sufuri ne a babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macao da ake kira Greater Bay Area. Hanyar ta kunshi bututu guda daya na karkashin ruwa, da gadoji biyu da tsibirai guda biyu da aka kafa, wanda ke zama daya daga cikin ayyukan hanyoyin da suka ratsa teku mafi kalubale a duniya.
An shirya bude hanyar da ta ratsa tekun don zirga-zirga a shekarar 2024. Kuma da zarar ta fara aiki, hakan zai rage lokacin tafiya tsakanin Shenzhen da Zhongshan, daga sa’o’i biyu a yanzu zuwa kusan mintuna 20 kacal.
Shugaban rukunin kula da harkokin zirga zirga na lardin Guangdong, Deng Xiaohua ya ce, hanyar Shenzhen zuwa Zhongshan, gami da gine-ginen da tuni aka samar, kamar gadar da ta hada Hong Kong-Zhuhai-Macao, za ta samar da tsarin hanyoyin tsallaka teku da ma kogi a yankin Greater Bay, wanda zai kara bunkasa hanyoyin zirga-zirga tsakanin biranen dake kewaye.(Ibrahim)