Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga kasashen duniya, da su dauki matakan gaggawa don magance rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Xi ya kuma bukaci kwamitin sulhun MDD, da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, tare da yin duk mai yiwuwa, wajen ganin an tsagaita bude wuta, da tabbatar da tsaron fararen hula, da kuma dakatar da bala’in jin kai.
Bugu da kari, ya kamata a gaggauta farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila, da hanzarta farfado da batun ’yancin al’ummar Palasdinu na kafa kasarsu ta kansu da ’yancinsu na yin rayuwa. Shugaba Xi ya bayyana haka ne a cikin sakon taya murna da ya aika wa taron MDD, wanda aka gudanar jiya Laraba, domin tunawa da ranar kasa da kasa ta nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu. (Ibrahim Yaya)