Don maganin hauhawar farashin da ake fuskanta a Nijeriya tare da rage wa ma’aikatansu radadin matsalar tattaln arzikin da ake ji a jiki, wasu kamfanoni sun kara wa ma’aikatansu albashi na kashi 18.35 cikin dari, wanda hakan ya kai na naira tiriliyan 29.45 a cikin wata shidan farko na shakarar 2023.
Wannan yana kunshe ne a rahoton Hukumar Kididdiga (NBS), ta kuma ce, kyautar kudi a mastayin tukuici da kamfanoni ke yi wa ma’aikata ya tashi daga naira tiriiyan 24.88 a zangon farko na shekarar 2022 zuwa naira tiriliyan 29.45 a zangon farko na shekarar 2023.
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
- An Haramta Shan Sigari A Wuraren Shakatawa Da Makarantu A Faransa
Wadannan kare-kare yana zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikata ke fuskantar tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashi a kasa.
Da take tsokaci a kan yadda tukuicin da ake ba ma’aikata ya karu, Hukumar NBS ta ce, “A zango na farko dana biyu, tukuicin ma’aikata ya karu da kashi 15.08 da kuma kashi 19.41 a cikin shekarar.
Hauhawar farashi ya sanya mafi karancin albashi na 33,000 ya rasa daraja da kashi 40 a cikin dari inda albashin ma’aikaci baya iya saya masa abincin da zai ciyar da iyalansa.