Babban bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da matakin haramta hada-hadar kudi a asusun ajiyar banki da babu BVN da lambar NIN daga watan Maris din 2024.
A wata takardar da aka raba wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kudi da masu gudanar da hada-hadar kudi, CBN ya ce za a hana amfani da asusun ajiyar.
- Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Cape Verde Da Ci 5-0
Babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne asusu ya zamana yana da BVN ko NIN.
CBN ya ce nan ba da dadewa ba za a gudanar da cikakken bincike kan asusun da babu BVN ko NIN, kuma da zarar an samu babu za a dakatar da asusun.
“Dukkan cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke jagoranta ana bukatar su yi aiki da tsauraran matakai kan takunkumi kan asusun ajiya,” in ji Efobi da Mustapha a cikin takardar sanarwar.