Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato a yau Juma’a ya gabatar da daftarin kudurin kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 270 a gaban majalisar dokokin jihar domin amincewa.
A cewar gwamnan kasafin kudin sabuwar shekarar na da manufar tabbatar da muradun al’umma a fadin jihar na wanzar da kudurorin gwamnatinsa na raya jiha ta kowane irin fanni.
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 1.8 Ke Dauke Da Cutar Kanjamau – Hukumar NACA
- CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024
A kasafin na 2024, kudin manyan ayyuka sun kama naira biliyan 90, 640, 286 a yayin da kudaden al’amurran yau da kullum suka kama naira biliyan 46, 923, 537, sai kudaden gudanarwa naira biliyan 50, 938, 232.
Fannin ilimi ya samu kaso mafi yawa na naira biliyan 42, 868, 402, sai fannin lafiya da ke biye da naira biliyan 31, 014, 441, a yayin da ma’aikatar ayyuka ta samu naira biliyan 18, 807, 208, sai fannin aikin gona da ke da naira biliyan 10, 252, 388 wanda ya hada da samar da nau’ukan abinci ga al’umma da takin zamani da kayan aikin gona ga manoma.
Gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa ta yi tanadi na musamman ga tallafa wa al’umma a kasafin kudin tare da yaki da fatara da karfafawa mata da matasa domin ganin sun zamo masu dogaro da kai.
A jawabinsa, shugaban majalisar dokoki ta jiha, Honarabul Tukur Bala ya tabbatarwa da gwamnan cewar majalisar za ta dukufa ga aikin tabbatar da kasafin kudin domin samun nasarar kudurorin gwamnatinsa.