A jiya Juma’a, gwamnatin kasar Argentina ta ba shugaban babban gidan rediyon da telabijin na kasar Sin CMG, Mista Shen Haixiong, wata lambar yabo.
Bisa amincewar shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez, an ba mista Shen lambar yabo ta “hadin gwiwa da musaya a fannin al’adu tsakanin kasashe daban daban”, don jinjina masa bisa dimbin gudunmowar da ya bayar wajen kara azama ga cudanyar da ake yi tsakanin jama’ar kasashen Argentina da Sin, a fannin al’adu, gami da zurfafa zumunta a tsakaninsu.
Gwamnatin kasar Argentina ta kan bayar da wannan nau’in lambar yabo ga manyan jami’ai na kasashe daban daban, wadanda suka ba da gudunmowa ga yunkurin karfafa amincewa da juna, da sa kaimi ga cudanyar al’umma ta fuskar al’adu, tsakanin kasar Argentina da sauran kasashe. (Bello Wang)