Hanyoyi Da Za Ku Bi Domin Sanya Hakoranku Su Rika Sheki
Fararen hokora na kara kwarin gwiwar magana a cikin abokai ba tare da jin kunya ba. Yawancin mutane ba su da masaniyar yadda za su magance matsalar rashin fararen hakora wasu har suna zaton halitta ne, to ga hanya mai sauki a da za a bi wajen magance matsalar cikin sauki
Hanyoyin su ne kamar haka.
Dabi’ar cin abinci
- Dole mutum ya canja dabi’arsa ta cin abinci, ma’ana mutum ya kasance yana cin abubuwa masu gina jiki, kuma yana da kyau ya guje wa cin abincin da yake da farin sukari a cikinsa (sugar). Ta’ammuli da abubuwan da suke hade da Madara, mini da kuma shan wadataccen ruwa mai tsafta duk suna inganta lafiyar hakuri.
- Amfani da Danko (Chewing gum)
Taunar Danko wato wanda akafi sani da ‘Chewing gum’ a turance yana taimaka wa matuka gaya wajan hana zaman wani abu a cikin sakon hakori, sanadiyyar hakan ka iya kawo tsutsen hakori dama sauran dangogin matsalolin da suka shafi hakorin baki daya.
- Sauya magogin baki (toothbrush)
Yana da matukar mahimmanci, wanke baki a kai -a kai domin yin hakan zai taimaka wajen fitar da duk wani nau’in abin da ya makale a hakorin. Haka zalika yana da kyau a ce mutun yana sauya magogin bakinsa duk tsawon wani lokaci (akalla duk bayan wata uku)