Gwamna Uba Sani ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafa wa nakasassu a jihar Kaduna, inda ya kara da cewa “babu ja da baya a kudurinmu na tallafawa nakasassu.”
Gwamnan wanda ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na tafiya da hada kan nakasassu a jihar, ya yi wannan jawabin ne a bikin ranar nakasassu ta duniya (IDPD).
- Guterres: Wajibi Ne Shugabannin Duniya Su Kawo Karshen Mummunan Dumamar Yanayi
- Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista
Uba sani ya ce, makomar nakasassu ta ta’allaka ne akan hada kan shugabanninsu da tafiya da su acikin tsarin tafiyar da gwamnati. Gwamnan ya kara da cewa, ajandar SUSTAIN na gwamnatinsa, ta tattaru ne kan tallafawa marasa karfi da masu bukata ta musamman kamar nakasassu.
Sanata Uba Sani ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su dinga amsa kiran Majalisar Dinkin Duniya na taron shekara-shekara kan tattauna batun nakasassu.