Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya musanta da kakkausar murya cewa, babu wani abu da ya amfana don gane da maido da lasisin kamfanin ‘Integrated Logistic Services Nigeria Limited (Intels)’ na lura da jiragen ruwa.
A wata wasika mai kwanan wata, 30 ga watan Nuwamba, da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Nijeriya, NPA ta aike wa dukkan kamfanonin jiragen ruwa da ke aiki a Nijeriya, ta bayyana cewa, ta mayar wa kamfanin ‘Intels’ lasisinsa da gwamnatin baya ta dakatar.
- Yadda Matakin Raya Kauyuka Da Sin Ta Dauka Ke Taimakawa Kawar Da Talauci Da Ma Yayata Aladun Kasar
- Yadda Na Hana ‘Yan Boko Haram Mayar Da Jihar Neja Hedikwatarsu – Tsohon Gwamnan Jihar
Da yake karin haske kan lamarin, Atiku Abubakar ya yi amfani da shafinsa na Facebook inda ya wallafa a ranar Lahadin da ta gabata kan rashin jin dadinsa na zarge-zargen cewa, ya amfana da maido da lasisin. Ya bayyana cewa, ya sayar da hannun jarinsa na kamfanin tun a watan Afrilun 2021 ga kamfanin Orlean Investment Group.
Atiku ya kara da cewa, “Kamfanin Intels ya kuma bayyana wa jama’a cewa, na sayar da hannun jarina na kamfanin, yanzun wasu ne ke kula da kamfanin ba ni ba”.