Gwamanan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ,Bola Ahmed Tinubu, ya amince zai dauki Musulmi a matsayin mataimakinsa.
BBC ta rawaito cewa, Ganduje ya yi wannan bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan malaman jihar kusan 100 suka kai masa ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar.
- Tinubu Gogaggen Dan Siyasa Ne, In Ji Ganduje
- Kotu Ta Hana Ganduje Ciyo Bashin Biliyan 10 Don Sanya CCTV a Kano
Gidan talabijin na Channel TV ya ambato gwamnan na cewa ”Mun ba shi shawara ya dauki Musulmi a matsayin mataimaki kuma ya amince, saboda ba wani abu ba ne sabo a Najeriya”.
Ya kumna yi kira ga taron malaman da su rika yi wa Tinubu addu’o’in samun nasara a zaben 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp