Mummunan harin bom da wani jirgin sojojin Nijeriya ya kai kan wasu masu bikin maulidi a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, ya tayar da hankulan jama’a tare da zaman zullumi musamman a jihar.
Jirgin sojin wanda aka ce mara matuki ne ya kai hare-haren bom a kan taron maulidin ne a ranar Lahadi da dare yayin da ake tsaka da taron maulidin.
- An Rufe Taron Fahimtar Sin Na shekarar 2023
- Gwamnatin Birtaniya Na Damuwa Kan Yadda Ake Neman A Mayar Da Kayayyakin Tarihi Da Ta Mallaka
Harin ya haddasa asarar rayukan mutane sama da 90, inda wasu kuma da dama suka ji raunuka.
Tun da farko dai, hedikwatar sojin saman Nijeriya ta musanta kai wannan hari bayan mai magana da yawunta, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana cewa jiragen yakinsu cikin sa’o’i 24 da suka gabata ba su kai wani farmaki ba a Jihar Kaduna.
Gabkwet, ya yi bayanin cewa ba sojojin sama ne kadai suke amfani da jirgin kai farmaki mara matuki ba cikin jami’an tsaron da ke fafatawa da ‘yan bindiga a Jihar kaduna,.
Sai dai daga bisani gwamnatin jihar ta ce sojojin kasa ne suka kai harin da yayi sanadin mutuwar sama da mutane fiye da 90 kamar yadda wasu jaridu suka ruwaito da safiyar yau a jihar.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce babban hafsan rundunar soji ta 1 ta Nijeriya da kwamandan rundunar Operation Whirl Punch, Manjo Jannr VU Okoro, sun bayyana cewar lamarin ya faru ne bisa kuskure yayin da rundunar sojojin ke ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda.