Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki yayi Allah-wadai da kashe mutane masu Maulidi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Wannan na cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan kafafen yada labarai, Abba Ibrahim Wada ya fitar.
- Dan Kwallo Ya Mutu Ana Tsaka Da Atisaye A Ogun
- Kaduna: Muna Neman Afuwar Kisan Masu Maulidi – Hafsan Sojin Kasa
Saraki, ya ce ya zama dole a yi bincike domin gano wadanda suka aikata wannan abu sannan a dauki matakin hana faruwar irin hakan a nan gaba.
“Kashe mutane ta hanyar harba musu bom da aka yi a lokacin da suke bikin Mauludi a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna abin takaici ne.
“Da ni da iyalina muna mika sakon ta’aziyyarmu ga al’umma da gwamnatin Jihar Kaduna da iyalan wadanda wannan ibtila’i ya fadawa.
“Ina addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu sannan wadanda suka samu rauni kuma Allah Ya ba su lafiya.
“Sai dai bayan wannan mummunan ibtila’i, ya zama dole mu gujewa faruwar irin wannan a nan gaba. Sannan akwai bukatar a gudanar da bincike domin a gano yadda wannan abin ya faru sannan a kawo hanyoyin gujewa faruwar hakan a nan gaba.
“Har ila yau, ya zama dole a sake nazari, wannan ya zama izina, bugu da kari a hada hannu waje guda wajen sake gina kishin kasa a zukatan mutane, adalci da kaunar juna domin tabbatar da kiyaye lafiyar duk wani dan kasa,” in ji Saraki.
A ranar Lahadin da ta gabata ne jirgin sojin Nijeriya ya jefa wa wasu mutane da ke gudanar da taron Mauludi bom, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 85 da kuma jikkata da dama.