Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta tsallake karatu na biyu kan daftarin kasafin kudin shekarar 2024 na Gwamna Abdullahi Sule na Naira biliyan 199.9.
Gwamna Sule ya gabatar da kudirin kasafin ga majalisar domin tantancewa da kuma amincewa a ranar 1 ga watan Disamba, 2023.
- Wang Yi: Sin Da Angola Sun Kafa Misali Na Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
- 2024: Majalisar Zartaswar Adamawa Ta Amince Da Kasafin Naira Biliyan 225
Kakakin Majalisar Danladi Jatau (Kokona ta Arewa, APC) ne ya sanar da amincewa da kudirin zuwa karatu na biyu a ranar Laraba.
Jatau ya bukaci kwamitin kudi da kasafi da ya yi aiki a kan kudirin sannan ya mika rahotonsa ga majalisar ranar 18 ga watan Disamba, 2023.
Ya kuma nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da ‘yan majalisar suka bayar a lokacin da ake tattaunawa kan kasafin kudin, ya kuma yi kira da a ci gaba da ba su goyon baya.
Bugu da kari, shugaban masu rinjaye na majalisar, Suleiman Yakubu Azara, ya bayyana batun kudirin, inda ya jaddada mayar da hankali kan yadda za a samu ci gaban tattalin arziki da ci gaban jihar.
Ya yaba wa Gwamna Sule bisa gabatar da kasafin kudin da zai magance kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Shugaban Masu Rinjaye ne ya gabatar da kudirin kudurin don daidaita karatu na biyu sannan shugaban marasa rinjaye Luka Iliya Zhekaba ya goyi bayan kudurin.
Mambobin majalisar daban-daban da suka hada da mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Oyanki, sun bayyana goyon bayansu ga kasafin.
Kwamitocin majalisar dokokin jihar Nasarawa na shirin fara gayyatar shugabannin ma’aikatu domin kare kasafin kudin a wani bangare na tsarin majalisar.