An fara aiki da wani dakin gwaje-gwajen kimiyya mai zurfin mita 2,400 a lardin Sichuan dake yankin kudu maso yammacin kasar Sin, wanda ya zama dakin gwaje-gwaje mafi zurfi da kuma girma dake karkashin kasa a duniya.
Masana kimiyya sun yi imanin cewa, dakin gwaje-gwajen ya samar musu da wani wuri mai “tsabta” don gano abubuwan da suka shige duhu. Sun kuma bayyana cewa, zurfin dakin gwaje-gwajen, yana taimakawa wajen toshe galibin kofofin da haske daga sararin samaniya ka iya shiga, wadanda ka iya lalata binciken da ake gudanarwa.
Dakin binciken dake karkashin kasa mai zurfi da kuma na’urorin kariya daga haske da ake kira (DURF) yana karkashin dutsen Jinping a yankin Liangshan Yi mai cin gashin kansa na lardin Sichuan. (Ibrahim Yaya)