Wasu masu binciken kudi na waje da kamfanin kera motoci na Volkswagen na kasar Jamus ya yi hayarsu, sun bayyana cewa, ba su samu wata shaidar dake nuna cewa, an tilastawa ’yan kwadago yin aiki a kamfanin dake jihar Xinjiang ta Uygur ta kasar Sin ba.
A cewar Markus Loening, mutumin da ya kafa kuma manajan daraktan Loening Human Rights & Business Business, ba su samu wata alama ko shaida ta tilasta wa ma’aikata yin aiki ba.
- Kasar Sin: Yawan Kunshin Kayayyaki Da Aka Isar A Kasar Ya Kafa Wani Sabon Tarihi
- An Bayyana Rawar Da Kasar Sin Ta Taka Kan Sauyin Yanayi Yayin Taron COP28
Kamfanin Volkswagen na hadin gwiwa da kamfanin harhada motoci na kasar Sin mai suna SAIC Motor Corporation Ltd wajen tafiyar da masana’antar.
Loening ya kara da cewa, “Mun duba kwangilolin aiki da tsarin biyan albashi na dukkan ma’aikata 197 a cikin shekaru uku da suka gabata, mun kuma yi tambayoyi 40, kuma mun sami damar duba masana’antar cikin ’yanci. Yana mai cewa, an kwatanta bayanan da aka tattara ta yadda za a samu dorewa da samun daidaito a tsarin.
A cewar kamfanin Volkswagen, rahoton da MSCI ESG ya wallafa mai kunshe da zarge-zargen take hakin bil Adama a jihar Xinjiang, “ba daidai ba ne, kuma baki dayansa yaudara ce.” Don haka, kamfanin Volkswagen yana daidaita wannan batu tare da MSCI. (Ibrahim Yaya)