Manzon Allah (SAW) Dan Makka ne, Allah ya zabar masa garin, saboda girmama garin ma Allah ya sa an gina masa daki a nan, don gimama garin Allah ya yi hakan ba don yana bukatar dakin ba.
Amma da mutanen garin suka yi kasassaba sai Manzon Allah ya koma Madina, shi ma Allah (SWT) ya ce ya koma can kamar yadda ya zo a cikin Suratun Nisa’i, “Duk wanda ya fito daga gidansa zai yi Hijira zuwa wurin Allah da Manzonsa”. Haka nan ma Annabi (SAW) ya fada a Hadisi, “Duk wanda Hijirarsa ta zama niyyarsa zuwa wurin Allah da Manzonsa…”, ma’ana idan mutum ya bar Makka zuwa Madina lokacin Hijra. Shi ya sa taba sha’anin Manzon Allah (SAW) yana da matukar hadari sosai.
Makka garin Allah ce, ga alhurmomin Allah nan, amma da Manzon Allah ya yi Hijira ya koma Madina, sai Allah ya ce duk wanda ya tafi can ya tafi wurinsa ne (SWT) domin girmama inda Annabi (SAW) ya koma.
Ko Kuma ayar tana nufin duk mutane ne, saboda Allah (SWT) ya aiko shi ne daga cikin mutane, ba aljannu ko mala’iku ko wata halitta daban ba.
Ayar da take nuna hakan ita ce ta cikin Suratul Bakarah, “Kamar yadda muka aiko a cikinku (‘Yan Adam duka) Ma’aiki maigirma daga cikinku ya zo ya karanta muku ayoyinmu, ya tsarkake ku, ya sanar da ku littafi da hikima, kuma ya sanar da ku abin da kuka kasance ba ku sani ba.”
Annabi (SAW) ne ya sanar da duniya kaf abin da ba ta sani ba.
A cikin mutane aka aiko shi amma kuma ba mutum ne kamar kowa ba. Ya fi mutane darajojin da ba za su kirgu ba, kankat ma babu wanda Allah ya zaba kuma yake so kamar sa (SAW).
Allah ya nada shi Manzon Rahama ne ga kowa da kowa, domin duk halitta ta samu wannan rahamar. Shi ya sa duk wanda aka raba shi da shi (SAW) sai ya zama ya fifita.
Wannan duka a bisa sabanin da aka samu ne a tsakanin masu Tafsirin Alkur’ani mai girma kan cewa wane ne ake nufi da “an aiko Manzo ne daga cikinsu?”. Duk wanda mutum ya dauka a nan, ya yi.
Babban abin lura a matakan mutanen da muka jero su dangane da wannan aya ta “Lakad ja’akum”, a kan kalmar “min anfusikum”, da kowanne ke cewa daga cikinsa ne aka aiko Annabi (SAW), shi ne fahimtar cewa Allah (SWT) ya yi haka ne don su san Annabi (SAW), su san darajarsa, su san gaskiyarsa.
Misali, ‘yan Makka da suke cewa da su ayar take magana, ai sun san gaskiyarsa. Domin lokacin da Annabi (SAW) ya ce musu Allah ya aiko shi da Musulunci, dattawan cikinsu masu hankali sun ce “mutumin nan fa tun yana yaro bai taba karya ba, sai yanzu ne da ya shekara 40 za a ce ya yi karya? Wallahi gaskiya ne abin da ya zo da shi”.
Wasu kuma suka ce “mutumin nan bai taba karya ba, bai taba yi wa ‘Yan Adam karya ba, don haka ba zai yi wa Allah karya ba,”.
A nan, ya tabbata cewa su mutanen Makka sun san gaskiyarsa, da amanarsa, saboda yarda da shi kan haka sun bashi ajiya da yawa duk da ba su son sa, fada suke yi da shi amma sun yarda da shi a matsayin mai amana. Abin mamaki, duk kayan ajiyarsu suna wurinsa, sai kuma suka taru za su kashe shi a cikin dare. Allah ya bashi mafita ta yin hijira zuwa Madina.
Ya kamata mu yi nazari sosai a nan dangane da gaskiya da amanar Annabi (SAW), mutanen da suka nemi kashe shi su ne kuma suke da ajiyar kayayyakinsu a wurinsa, sannan cin kayan abokan gaba na yaki halal ne; amma da ya tashi zai tafi sai bai tafi musu da kayansu ba, haka ya tsallaka ya bar musu. Ya kira dan’uwansa Sayydina Aliyu (Karramallahu waj’hahu) ya damka masa amanonin (kayan ajiyar) ya ce ya mayar musu, bayan kwana uku shi kuma ya biyo shi Madina.
Da gari ya waye wasu suka tambayi labari, aka ce musu ai ya fita ya bar gari, suka ce ina kayan da suka bashi ajiya, aka ce ya bar dan’uwansa ya mayar wa kowa kayansa, ka ga a nan wani zai san addininsa shi ne gaskiya, domin wanda suke gaba da shi sannan ga kayansu a hannunsa amma bai tafi da su ba, ya bar musu tabbas mutum ne mai gaskiya ba kamar sauran mutane ba.
Larabawa ba su taba zargin Annabi (SAW) da karya ba tun a zamanin jahiliyyarsu, ba su taba zarginsa da barin nasiha ba gare su, kasancewar a cikinsu ya rayu, wasu ma a gaban su aka haife shi, tun yana yaro sun san kuruciyarsa, samartakarsa da gwarzantakarsa, amma duk irin halayen shashanci na samari bai taba yi ba (SAW). Ta fannin Larabawa kenan.
Idan kuma aka dubi cewa Allah (SWT) ya raba Annabi (SAW) a cikin ‘Yan Adam ne bakidaya, ma’ana fassarar “min anfusikum” da ke nufin “mutane bakidaya”, to ya yi haka ne don Rahamar Annabin ta shafi mutane duka don mu samu falala.
Babu wata kabila a doron kasa ta Larabawa da ba ta da dangantaka ta jini da Manzon Allah (SAW) ta wurin kakanni ciki har da wadanda ake gani makiyansa ne. Misali, Umayyawa suna da dangantaka da shi (SAW) ta kakanni, idan aka dubi Abu Dalib (dan’uwan mahaifin Annabi SAW) za a ga cewa shi sa’an Abu Sufyanu ne. Mahaifin Abu Dalib shi ne Abdulmuddalibi dan Hashim, dan Abdumanafi. Shi kuma Abu Sufyanu dan Harbu, dan Umayyata, dan Abdumanafi. Ka ga a nan, sun hada kaka daya. Shi ya sa a ranar Fatahu Makkah da Sayyidina Umar (RA) yana neman a bashi izini ya kashe Abu Sufyanu, sai Sayyidina Abbas (RA) ya ce ma sa “mu kake so ka yi wa haka, don ka san -shi- ba baniy Adiyyi ba ne, baniy Abdumanafi ne”. Ma’ana Abbas yana kare ma Abu Sufyanu don kasancewarsa dan gidansu.
Shi ya sa duk Kabilar Larabawa ke takama da cewa sun hada dangi da Annabi (SAW) ta wani wuri, kuma wannan zai amfane su.
Domin kara fayyace kusancin da dukkanin wadannan matakai ke nema da Annabi (SAW), Abdullahi bin Abbas (RA) ya tafi a kan cewa ayar nan da ta ce “Ka ce ni ba na neman wani Lada a cikin isar da sakon nan, sai dai nuna soyayya ga makusantana”, tana nufin kira ne ga duk danginsa da su Larabawa su so Manzon Allah (SAW) saboda kusancinsa da su.
Dalilin saukar ayar shi ne, wasu ne daga cikin Sahabbai (RA) suka hada kudi mai yawa suka ba Manzon Allah (SAW) a matsayin tukwicin sakon Musuluncin da ya kawo, sai Allah ya ce a mayar musu, Manzon Allah don Allah ne ya kawo sakon ba don su biya ba.
Manzanni ba su rokon a biya su ladan sakon Allah da suke isarwa kuma su shiryayyu ne.
A kan wancan maz’habar ta Abdullahi bin Abbas (RA), Imamu Bukhari da Muslim sun ruwaito Hadisi a kai daga Muhammadu bin Basshari, daga Muhammadu bin Ja’afari, daga Shu’ubatu, daga Abdulmaliki bin Maisarata ya ce, “Na ji Dawusu (Almajirin Abdullahi bin Abbas) yana fada cewa an tambayi Abdullahi bin Abbas (RA) shin mecece fassarar ayar da ta ce “ba na neman Lada daga gare ku, sai dai soyayya a cikin dangina?”, sai Sa’idu (wani malamin Kuraishawa) bin Jubairu bin Mud’amu bin Adiyyi ya yi sauri (kafin Abdullahi bin Abbas ya ba da amsa) ya ce “abin da ake nufi da dangi makusanta su ne iyalan gidan Annabi (SAW), sai Abdullahi bin Abbas ya ce ma sa “ka yi gaggawa, babu wani dangi na Kuraishawa face Manzon Allah (SAW) yana da kusanci da su, abin da ayar take nufi shi ne “sai dai ku sada abin da yake tsakanina da ku na zumunta.”
Ibin Hajaral Askalani ya ce wannan fassara ta Sa’idu bin Jubairu ita ce wadda Aliyu bin Hussain (Zainul Abidiyn RA) yake kai, haka nan galibin malamai, ma’ana ana nufin a so iyalan gidan Manzon Allah (SAW).
Manzon Allah (SAW) yana da dangi da yawa, amma babu wadanda suka fi alfahari da shi kamar ‘ya’ya musamman wadanda suka fita daga jikinsa (SAW).
Baya ga Aliyu Zainul Abidyn da ke kan wancan fassarar, Malamai irin su Saddi da Amru bin Shu’aibin duk sun tafi a kai kamar yadda Imamud Dabari ya fitar daga gare su.
Idan an dauki fassarar da Sayyidina Aliyu Zainul Abidiyn (RA) ya tafi a kai ne, to ayar tana kira ne ga dukkan duniyar musulmi su so dangin Annabi (SAW) makusanta. Idan kuma fassarar Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA) aka dauka, to magana ce ake yi da Kuraishawa wadanda Annabi (SAW) ya fito daga cikinsu, ma’anar “min anfusikum” na cikin “Lakad ja’akum”.
Idan kuma an dauki cewa ayar da Muminai take magana a matsayin makusanta, to ko wane Mumini ya shiga cikin makusantan Annabi (SAW), saboda Manzon Allah (SAW) ya ce wa Salmanul Farisi yana daga cikin iyalan gidansa. Don haka kowane Mumini shi ma yake alfahari da cewa daga cikinsu ne Manzon Allah ya fito.