A wannan makon ne Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta bayyana cikakken dalilan da suka sa Ma’aikatan Tattalin Arzikin Teku ta amince da sake dawo da kwangilar kamfanin ‘INTELS Nigeria Limited’ na kula da kananan jiragn ruwa a tashoshin jiragen ruwan Nijeriya.
Sanarwar da ta fito daga hukumar gudanarwar NPA ta ce, ya zama dole a wayar wa da al’umma kai a kan lamarin da ya shafi dawowar kwangilar kamfanin na INTELS tun bayan da manajan tashar jiragen ruwa na Legas da ke Apapa ya fitar da sanawar dawowa da INTELS din.
- Atiku Ya Musanta Amfana Da Maido Da Lasisin Kamfanin Intels Da Gwamnati Ta Yi
- Kifewar Kwale-kwale Na Ci Gaba Da Salwantar Da Rayukan ‘Yan Nijeriya
Hukumar ta kuma ce, kamfanin INTELS ya sahhale wa gwamnatin tarayya fiye da Dala miliyan 193 a kokarin ganin an yi sulhu a kan dambarwar kwangilar.
Sanarwa ta kuma ce, gwamnatin tarayya ta yi asarar makudan kudade a matsayin kudin shiga a tsawon lokacin da NPA ta karbi ragamar tafiyar da kula da kananan jiragen ruwa a tashoshin, ta kuma kara da cewa, Nijeriya za ta yi tsimin fiye da Dala miliyan 326.895 sakamakon yarjejeniyar da aka cimma na dawo da INTELS a wannan karon.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, bayan da NPA ya karbi ragamar tafiyar da ayyukan INTELS an samu raguwa a bangaren kudaden shiga saboda rashin kayan aikin tafiyar da harkokin kula da kananan jiragen Ruwan.
A saboda haka an cimma wannan yarjejeniyar ne don kishin Nijeriya, kuma za a samu karin kudaden shiga a asusun gwamnatin tarayya sakamakon wannan kokarin.
Daga nan, hukumar NPA ta yaba wa Ministan harkokkin tattalij azikin teku, Adegbeyega Oyetola a kokarinsa na ganin an warware wannan dambarwar.
Oyetola, bai ji dadin yadda aka yi wa Nijeriya asarar kudaden shiga, a kan haka ya tabbatar da an warware lamarin.