Kakakin hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng ya bayyana yau Lahadi cewa, yanzu yawan kananan yaran da ke fama da cututtukan da ke shafar sassan dake taimakawa numfashi, ya ragu a duk fadin kasar Sin, bisa alkaluman da aka samu daga asibitocin kasar. Kana yawan kananan yaran da suke zuwa ganin likita ya dan ragu a yawancin manyan asibitoci da cibiyoyin kula da kananan yara da ke manyan asibitocin kasar.
A yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau, Mi Feng ya ce, a ’yan kwanakin baya ne yawan wadanda suka je ganin likita sakamakon kamuwa da cututtukan da ke shafar sassan jiki masu taimakawa numfashi bai karu sosai ba a kasar Sin, kuma ana ba da jinya gare su yadda ake bukata. (Tasallah Yuan)