Kwanaki uku bayan da wani kwale-kwale ya kife da fasinjoji 17 da mutuwar mutum biyu a ciki, wani kwale-kwalen ya sake kife wa da wasu mutum 16 a ranar Juma’a wanda aka gaza gano inda suka shiga.
A sanarwar manema labarai da Janar-Manaja na hukumar kula da jiragen ruwan Nijeriya (NIWA) a jihar Legas, Sarat Braimah, ta ce, jirgin ruwan ya tashi daga Mile 2 zuwa Ibeshe a garin Ojo da ke jihar Legas ne.
- Masana’antar Kannywood Ta Girgiza Da Rasuwar Daraktan ‘Izzar So’
- Sarkin Kano Ya Haramta Hawan Dawakin Matasa
A cewarta, kwale-kwalen ya karya ka’idojin tukin jiragen ruwa na yin tafiya a makare wanda ya fara tukin karfe 7:45 na dare, ta ce, a lokacin da jirgin ke tafiya ne guguwar iska ta ja shi inda ya ci karo da wani da ke tsaye wanda hakan ya janyo kifewarsa.
Ta ce, “Mun samu rahoton hatsarin kwale-kwalen ‘A W19’ dauke da mutum 16 a ciki a kan hanyar Ojo da ke jihar Legas. Kwale-kwalen ya taso ne daga Mile 2 zuwa Ibeshe ya nutse cikin ruwa bayan karya dokar tuki na tafiya cikin dare.
“Dukkanin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen ciki har da yara kanana basu sanya rigar kariya ba.”
Ta ce, sun tura jami’ansu wurin da lamarin ya faru domin aikin ceto, “jami’anmu sun shafe awanni suna nemansu amma ba su same su ba, ko da yake har yanzu ana ci gaba da nemansu.
“Kwale-kwalen yanzu haka yana hannun ‘yan sanda a Marine.”