Jakadan Falasdin a Nijeriya, Abu Shawesh ya bayyana cewa sojojin Isra’ila ta kama yara 245, mata 147, ‘yan jarida 41 da wasu 1,666 bayan tsagaita wuta na kwanan nan a Yammacin Kogin Jordan.
Jakadan Falasdin ya bayyana hakan ne a wani taron ‘yan jarida da ya kira a ofishin jakadancin qasar da ke Abuja a yau Litinin.
- Jakadan Sin Ya Bayyana Matsayin Kasar Sin Da Matakanta Da Ra’ayinta Kan Batun Falasdinu Da Isra’ila
- Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Dabarun Warware Rikicin Isra’ila Da Falasdinawa
A cewarsa, ko a ranar 7 ga Oktoba a yankin Yammacin Kogin Jordan, sai da sojojin Isra’ila ta kasha Falasdinawa guda 243 ciki har da yaea 65.
Ya kara da cewa yawan Falasdinawan da ake kashewa lamari ne mai ban mamaki da takaici idan aka kwatanta da kasashen da ke da yawan al’umma. Ya ce a cikin kasa mai yawan jama’a da suka kai miliyan 220, an halaka kusan kashi miliyan 2.2. Inda ya ce wannan lamari ne mai tayar da hankali idan aka duba yawan adadin mutanen da aka kashe.
“Ko a ranar 28 ga Nuwamba, a ranar da aka tsagaita wuta, likitocin da aka tilasta musu barin cibiyar lafiya ta AL-Nasr da ke Gaza, wanda suka bar jaririn ba tare da kulawa ba. Bayan dawowarsu, sun tarar da jarirai 5 sun mutu. Hotuna da bidiyo sun karade kafafan yada labarai da ke nuna yadda jikinsu ke ta rubewa,” in ji jakadar Falasdin