Gwamna Dauda Lawal ya jajanta wa al’ummomin da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a baya-bayan nan, ya kuma yaba wa sojoji bisa kokarinsu.
Akwai rahotanni masu kyau da yawa na kawar da dimbin ‘yan bindiga a Zamfara da sauran dazuzzukan Arewa maso Yamma.
- An Shiga Firgici Bayan Sabon Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Gwamnatin Adamawa Ta Rantsar Da Sabbin Kantamomin Raya Karkara 50
A wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamna Lawal ya nuna matukar damuwarsa kan hare-haren da aka kai a karamar hukumar Zurmi.
Ya ce duk da hare-haren da ‘yan bindigar ke kai wa, rahotanni masu inganci sun nuna an kawar da fitattun shugabannin ‘yan bindigar da ke aiki a jihar Zamfara.
Sanarwar ta kara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta damu matuka da hare-haren baya-bayan nan da ake kaiwa al’umomin jihar, musamman a kananan hukumomin Zurmi, Maru, da Tsafe.
“Muna mika ta’aziyyarmu ga daukacin al’ummar karamar hukumar Zurmi, musamman iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa ‘yan uwansu.
“Gwamnatin jihar za ta bayar da tallafi da kayayyakin agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa, muna so mu tabbatar wa al’ummar Zamfara cewa mun jajirce wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu.
“Muna sane da sadaukarwar da jami’an tsaro suka yi a kokarin da suke na kare rayukan al’umma, gwamnatin jihar za ta ba su duk wani kayan aiki da kuma tallafin da ya dace domin yakar ‘yan fashi, ba za mu huta ba har sai Zamfara ta samu cikakken tsaro.
Gwamna Lawal ya kuma yabawa kokarin jami’an tsaro na kawar da dimbin shugabannin kungiyoyin ‘yan bindiga a fadin jihar.
“Mun samu rahotanni masu kyau na ci gaban da sojoji suka samu a yakin da ake da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, kokarin da jami’an tsaro suka yi da sadaukarwar abin a yaba ne, dole ne mu ba su goyon baya da kuma yi musu addu’a.
“A cewar rahotannin tsaro, sojojin sun yi nasarar kawar da Kachalla Ali Kawaje, sarkin ‘yan bindiga da ya kitsa sace daliban jami’ar tarayya ta Gusau.
“An samu nasarar kawar da barayi a wurare daban-daban da suka hada da Danjibga, dajin ‘Yar tsakuwa, dajin Munhaye, dajin Kauran Zomo, dajin Dansadau, da kauyen Akuzo.
“Wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindigan da aka kashe sun hada da Kachalla Jafaru, Kachalla Barume, Kachalla Shehu, Tsoho, Kachalla Yellow Mai Buhu, Yellow Sirajo, da Kachalla Dan Muhammadu.
“Sauran sun hada da Kachalla Makasko, Sanda, Abdulbasiru Ibrahim, Mai Wagumbe, Kachalla Begu, Kwalfa, Ma’aikaci, Yellow Hassan, Umaru Na Bugala, Isyaka Gwarnon Daji, Iliya Babban Kashi, Auta Dan Mai Jan Ido, Yahaya Dan Shama.”