Firaministan Jamhuriyar Kongo Anatolc Collinet Makosso, ya bayyana cewa, kasar Sin aminiyar kasarsa ce. Kuma a duk lokacin da kasarsa ke fama da wata matsala, kasar Sin ba ta dakatar da samar da goyon baya da tallafi. Don haka har abada, jama’ar kasarsa ba za su manta da wannan ba.
Firaminista Makosso ya yi wannan furuci ne lokacin da sabuwar jakadiyar kasar Sin dake Jamhuriyar Kongo Madam Li Yan ta ziyarce shi a jiya Talata, bayan da ta kaddamar da aikinta na wakilcin kasar Sin ba da dadewa ba, inda ya kara da cewa, a cikin shekaru kusan 60 na hadin gwiwar kasarsa da Sin, sassan biyu sun kulla huldar diplomasiyya, da sada dankon zumunci a tsakaninsu kamar ’yan uwa. Kaza lika a sabuwar shekarar da ke tafe, kasarsa na son yin kokari tare da Sin, wajen daukaka ci gaban muhimmin hadin kansu, da ciyar da dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni zuwa gaba.
A nata bangaren kuwa, jakadiya Li Yan ta bayyana cewa, a cikin ’yan shekarun da suka gabata, an raya dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Jamhuriyar Kongo bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni kamar yadda ya kamata, inda aka samu sabbin sakamako. Kuma ana sa ran ganin yadda bangarorin biyu za su yi kokari tare, wajen aiwatar da manyan ra’ayoyin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da inganta hadin kansu karkashin inuwar shirin “ziri daya da hanya daya” da tsarin FOCAC, a kokarin daga dangantaka a tsakaninsu zuwa babban matsayi. (Kande Gao)