Al’ummar birnin Nanjing sun yi shiru na wani dan lokaci, kuma an ji karar jiniya a ko’ina cikin birnin, yayin da a yau Laraba kasar Sin ke gudanar da bikin nuna alhini ga mutane dubu 300 da aka halaka, a kisan kiyashin da aka yi a Nanjing.
A shekarar 2014, babbar majalisar dokokin kasar Sin ta kebe ranar 13 ga watan Disamban ko wace shekara, a matsayin ranar tunawa da mutanen da aka kashe a birnin Nanjing, wanda ya faru a lokacin da sojojin kasar Japan suka kwace birnin a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937. Maharan Japanawa sun kashe Sinawa fararen hula da sojoji da ba su da makamai a hannunsu kimanin dubu 300 a cikin sama da makonni shida, wanda ke nuna daya daga cikin mafi girman danyen aikin da aka aikata a yakin duniya na biyu.(Ibrahim)