Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce ta kashe ‘yan bindiga 13 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kubutar da mutane 268 da aka yi garkuwa da su a wasu samame da hukumar ta kaddamar daga watan Yuni zuwa Satumba na 2023.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ta ce, an kama kimanin mutane 104 da ake zargi da aikata laifin fashi da makami, sannan kuma rundunar ta kama 97 da ake zargi da laifin kisan kai.
- Kowacce Yarinya Za Ta Samu Ilimi Da Sana’a A Jihar Katsina – Gwamnati
- An Shiga Firgici Bayan Sabon Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Ya kara da cewa, an kama mutane 148 da ake zargi da laifin aikata fyade, sannan kuma an kama mutane bakwai da laifin mallakar haramtattun kwayoyi.
Rundunar ta bayyana cewa, ta kuma kama bindigar fistul kirar waje guda daya da harsasai 523.
ASP Aliyu ya ci gaba da bayyana sauran kayayyakin da aka kwato da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda hudu, bindigu na gida guda shida, dabbobin da aka sato fiye da 600, babura 12 da wayoyin hannu guda 17.