Bayan sauke shugabannin hukumomi daban-daban, gwamnatin tarayya ta kori daraktocin hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN), hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NIMET), hukumar kula da sararin samaniyar Nijeriya (NAMA), hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) da Ofishin Tsaro da Bincike na Nijeriya (NSIB).
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ofishin yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar sufurin jiragen sama da kula da sararin samaniya ta tarayya, Odutayo Oluseyi a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba a Abuja.
- Sanatoci Sun Nemi A Rufe Hukumar AMCON Bayan Bacewar Naira Biliyan N146 Cikin Shekara Daya
- Kamfanin NNPCL Ya Zuba Naira Tiriliyan N4.5 Cikin Watanni 10 A Asusun Gwamnati – Kyari
Sanarwar ta ce, dukkan sakatarorin hukumomin da masu ba da shawara kan harkokin gudanar da hukumomin, ba sa cikin wadanda umurnin sallamar daga bakin aiki ta shafa.
Gwamnati ta umurci daraktocin da abin ya shafa da su mika ragamar ayyukan ofisoshinsu ga babban jami’in gudanarwa na hukumominsu.