Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe ta sanar da sauya jadawalin zabukan kananan hukumomi a jihar.
Dr. Mamman Mohammed, Shugaban Hukumar ne ya bayyana hakan a yayin taron masu ruwa da tsaki a zaben kananan hukumomin Jihar Yobe a ranar Alhamis.
- Gwamnatin Kano Za Ta Biya Wadanda Ta Yi Wa Rusau Diyyar N3bn
- Yadda Matashi Ya Yi Yunƙurin Hallaka Matarsa Don Ya Samu Damar Sace Mata Talabijin
Ya ce, “Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya yi godiya ga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar da ta sauya ranar zaben shugabanni 17 da kansiloli 178 na kananan hukumomin Jihar Yobe zuwa ranar 25 ga watan Mayu 2024.
“Hakan ya yi daidai da tanadin sashe na 197 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Maza da mata ‘yan jaridunmu za su tabbatar da cikakken yada bayanai ga masu zabe a Jihar Yobe.”
Mohammed ya jaddada cewa za su yada bayanai ga duk masu kada kuri’a a Jihar Yobe.
Ya kuma bayyana bukatar samar da tsaro a dukan rumfunan zabe a lokacin zaben.
Mohammed ya bayyana cewa, za a samar wa jam’iyyun siyasa ka’idojin zabe don tantance ‘yan takara.
Da yake jawabi ga jami’an zaben, ya bukace su da su kara himma wajen ganin an gudanar da zaben cikin nasara.
Mohammed ya bayyana amincewarsa ga masu ruwa da tsaki, inda ya jaddada kudurinsu na hadin gwiwa wajen cimma nasara.
Ya ce, “Ga ma’aikata na da jami’an zabe, dole ne ku rubanya kokarinku don ganin an samu nasara a zaben. Ina da yakinin ku masu ruwa da tsaki cewa hannayenmu za su kasance a kan tudu domin cimma kyak
“Don haka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jiha za ta dauki nauyin gudanarwa, tsarawa da kuma kula da zaben kansilolin kananan hukumomi.”