Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan zuri’ar Sabah mai mulki, gwamnati da al’ummar kasar Kuwait bisa rasuwar Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah.
Sanarwar mika ta’aziyyar na kunshe cikin wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Asabar a Abuja.
- Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf Ya Rasu Yana Da Shekaru 86, An Naɗa Meshaal A Magajinsa
- Tinubu Ya Zama Gwarzon Shekara Na Kamfanin LEADERSHIP
Da yake yaba wa da nasarorin da marigayi Sarkin ya samu cikin kankanin lokaci, Tinubu ya bayyana sarkin a matsayin mutum mai tausayi, zaman lafiya da jin kai, wanda ya yi afuwa ga fursunonin siyasa da ‘yan adawa, inda ya samar da ci gaba da kwanciyar hankali a fadin kasar.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa Majalisar zartarwar Sabah mai mulki, da duk wadanda suka yi alhinin rashin rashi tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya jikansa da rahama, ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi.