Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ba zai yiwu ‘yan wasansa su dora alhakin gaza lashe wasaninsu na baya -bayan nan kan rashin sa’a ba, bayan da ssuka buga kunnen doki da Crystal Palace a ranar Asabar.
Manchester City na kan gaba a wasan da ci 2 babu ko daya har zuwa lokacin da ya rage saura minti 15 a tashi wasan, amma ‘yan wasan Palace, Jean-Philippe Mateta Michael Olise suka farke kwallayen.
- Nijar Ta Cika Shekaru 65 Da Samun ‘Yancin Kai
- Kayan Masarufi Sun Sake Tashin Gwauron Zabi A NijeriyaÂ
Wannan ne karo na hudu a cikin wasanni shida da Manchester City ke yin canjaras bayan sun shiga gaba a wasan, lamarin da ya sa yaannzu Liverpool ke gabansu da maki uku, kuma suna da kwanten wasa guda daya.
Guardiola ya ce lallai ba rashin sa’a ba ce, sakamakon ya dace da irin kokarin da ‘yan wasansa suka yi.
Manchester City, wadanda suka yi wannan wasa ba tare da dan wasan gabansu, Erling Halaand ba, sun kai harin cin kwallaye har sau 19, idan aka kwatanta da na takwarorinsu, wadanda suka kai 5.