A yankin Asokoro na birnin Abuja hedkwatar kasar Najeirya, akwai wani titi mai suna “Titin Deng Xiaoping”. Marigayi Deng Xiaoping shi ne ya samar da tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje da gwamnatin Sin ta dade tana daukawa, kuma ga shi an rada wa titin sunansa, muna iya ganin cewa, ci gaban da aka samu karkashin wannan tsari na burge jama’ar wurin.
Ina dalilin hakan kuma? Idan an duba wasu ayyukan more rayuwa da kamfanonin Sin suka ba da taimako wajen gudanarwa, sun kasance sakamakon hadin gwiwa na karkashin wannan tsari. Alal misali layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna, tashar ruwa mai zurfi ta Lekki, da sabon filin jiragen sama na Abuja, da madatsar ruwa ta Zungeru da sauransu. Kuma ba a Nijeriya kawai ba, ana iya ganin irin wannan aiki a fadin nahiyar Afrika.
Bana ake cika shekaru 45 da aiwatar da wannan babban tsari na yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, wanda ya haifar da nasarorin a zo a gani, wanda kuma ya sa kasashen duniya, musamman ma kasashen Afrika su more ci gaban da kasar Sin ke samu.(Mai zane da rubutu: MINA)