Shugaban kasar Masar mai ci, Abdel Fattah al-Sisi, ya samu nasarar sake lashe zaben shugaban kasar Masar a karo na uku da aka gudanar, inda ya samu kashi 89.6% na kuri’un da aka kada a cewar sanarwar da hukumar zaben kasar ta fitar.
El-sisi ya fafata da ‘yan takara uku daga jam’iyyun adawa, inda babban abokin hamayyarsa ya samu kashi 4.5% na kuri’un. Sai dan takarar jam’iyyar adawa, Ahmed Tantawy da ya janye gabanin zaben saboda matsin lambar da ya fuskanta a yayin yakin neman zabensa.
Al-Sisi, mai shekaru 69, ya fara aiki a shekarar 2014, bayan rawar da ya taka wajen hambarar da wanda ya gaji buzunsa, shugaban masu kishin Islama, Mohammed Morsi a zaben da ya sake tsayawa takara a shekarar 2018 da kuma wannan nasarar da ya samu a wannan zaben zai tabbatar da zamansa shugaban kasa har zuwa 2029, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.