Jita-jita da wasu ke yadawa wai, masu jarin wajen na janyewa daga kasar Sin ko kadan ba gaskiya ba ne.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya majalisar gudanarwar Sin ta fitar wasu dokoki da suka shafi yadda za a kara jawo jarin waje da ma cin gajiyarsa yadda ya kamata. Dokokin sun bukaci da a inganta yanayin da ake ciki a cikin gida da waje, da bunkasa yanayin kasuwar da babu kamarta a duniya, wanda kuma za ta dace da yanayi na kasuwaci, bisa doka da ka’idoji na kasa da kasa.
- Sin Ta Kara Tallafin Kudi Don Maido Da Wuraren Kiyaye Ruwa A Yankunan Da Girgizar Kasar Ta Shafa
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kaucewa Aiwatar Da Matakan Da Ka Iya Barazana Ga Tsaronta
Ita ma hukumar dake tsara harkokin tattalin arzikin kasar Sin ta bayyana a yayin wani taro cewa, za ta himmatu wajen kara ci gaba da yin gyare-gyare, da nacewa kan ka’idar tabbatar da bunkasar tattalin arziki yadda ya kamata a matsayin babban fifiko, da neman ci gaba, yayin da ake tabbatar da daidaito.
A cewar taron, hukumar raya kasa da yin gyare-gyare, wadda ke tsara bunkasar tattalin arziki, ta bayyana ayyuka shida a wurin taron, wadanda suka hada da ka’idojin tafiyar da harkokin kudi, inganta amfani da kayayyaki da kara zuba jari, tallafawa ayyukan samar da kayayyaki da hidima, zurfafa gyare-gyare da bude kofa, karfafa ginshikin tsaron tattalin arziki, da tabbatar da kyautata jin dadin jama’a.
Bugu da kari taron ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da samar da damammaki, da kuzari, kuma tushen tattalin arzikin kasar na dogon lokaci bai canza ba.
Sanin kowa ne cewa, akwai dimbin damammaki na harkokin kasuwancin duniya a babbar kasuwar kasar Sin, da cikakken tsarin masana’antu, da sabbin hanyoyin bunkasuwa.
Alkaluma na nuna cewa, GDPn kowane mutum a kasar Sin, ya zarce dalar Amurka dubu 12, kuma rukunin masu matsakaicin kudin shiga, ya zarce miliyan 400, wanda ya samar da babbar kasuwar cikin gida mai dimbin damammaki. Kasar Sin ita ce kasa daya tilo da ke da dukkan nau’o’in masana’antu da MDD ta lissafa, kuma fa’idar da take da su a masana’antu, ba za a taba hada su da na sauran kasashe ba.
A makon da ya gabata ne kuma, aka gudanar da babban taron kolin raya tattalin arziki na shekara-shekara, don yanke shawarar ba da fifiko kan ayyukan raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2024. Kuma a yayin taron, shugabannin kasar Sin sun yi alkawarin fadada bude kofa mai inganci ga kasashen waje. Don haka, yada karya game da janyewar jarin waje a kasar Sin, labarin kanzon kurege ne, wanda ba shi da wani tushe, balle madafa. (Ibrahim Yaya)