Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta ce, ta kama wasu mutane biyar da aka samu da makamai da bindigu kirar AK 47 ba bisa ka’ida ba a kauyen Kurmi da ke karamar hukumar Bakori.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Katsina.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 4, Sun Sace 8 A Katsina
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 13, Sun Ceto Mutane 268 A Katsina
“A ranar 19 ga watan Disamba, 2023, mun samu bayanan sirri daga jami’anmu da ke hedikwatar ‘yan sanda reshen Bakori, tare da hadin guiwar ‘yan banga a lokacin da suke sintiri sun yi nasarar gano tare da kama mutane biyar.
“Wadanda ake zargin sun hada da Sharhabilu Dahiru, dan shekara 20 da Abubakar Tukur, 25 da Kasamanu Abdullahi, 20 da Abdulrahman Shu’aibu, 20, da kuma Sulaiman Sanusi, mai shekara 20.
“Dukkan wadanda ake zargin ‘yan kauyen Kakumi ne da ke karamar hukumar Bakori,” cewar Sadiq-Aliyu.
Ya kara da cewa da aka yi musu tambayoyi, nan take wadanda ake zargin suka amsa cewa sun sace makamin ne a gidan wani Jamilu Lawal da ke kauyen.
“Saboda girman laifin, nan take aka gayyaci Lawal din da bayar da umarnin ci gaba da bincike kan mallakar bindigar AK 47 ba bisa ka’ida ba.
“An ci gaba d tsare dukkan wadanda ake zargi da laigin yayin da ake ci gaba da bincike,” Cewar kakakin ‘yan sandan jihar.