A ranar Talata da dare ne, aka shirya bikin nuna wani fim mai taken “Peking Man, The Last Secret of Humankind” karo na farko, a hedkwatar Hukumar raya Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta MDD wato UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa. An dauki wannan fim din ne bisa hadin gwiwar Babban Gidan Rediyo Da Talabijin Na Kasar Sin wato CMG da Gidan talabijin na kasar Faransa wato France Télévisions da sauransu. Mataimakin shugaban sashen fadakar da jama’a na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta bidiyo a yayin bikin. Mataimakin babban darektan hukumar UNESCO Qu Xing da sauran wasu wakilan kasar Sin da na kasar Faransa sun halarci biki, tare da ba da jawabai.
An dauki fim din ta hanyar amfani da sabbin fasahohi na kasar Sin da kasar Faransa, domin nuna tarihin mutanen Beijing na can can can da, kuma shi ne fim na farko da ya nuna tarihin sauye-sauyen bil Adama a gabashin Asiya. Za a fara nuna fim din a hukumance a tashar shirin gaskiya na CMG da tashar talabijin ta France Télévisions 2 a shekarar 2024. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)