Babban da ga shahararren jarumin fina finan Hausa Rabilu Musa Ibro, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekaru 9 da suka gabata, Hanafi Rabilu Musa Ibro ya bayyana yadda har yanzu suke amfanuwa da zaman arziki da mahaifinsu ya yi da mutane a lokacin da yake raye.
Hanafi wanda shima ya shiga harkar barkwanci ya kuma bayyana cewar duk da cewar mahaifin nasu ya dade da rasuwa amma har yanzu mutane suna ci gaba da yi masa addu’oin samun rahamar Ubangiji.
- Manoma 40,000 Za Su Amfana Da Takin Zamani Na Bunkasa Noman Rani A Filato
- An Fara Gina Cibiyar UHD Highland Ta CMG
Inda ya kara da cewar iyalan marigayi Ibro suna matukar jin dadi idan suka ji ana yi wa mamacin addu’ar samun rahamar Ubangiji.
A kowane lokaci mu kan ji ko kuma a fada mana cewar mahaifinmu ya samu kyakkyawan yabo a wajen mutanen da ya yi mu’amala dasu da kuma wadanda yake sakawa nishadi.
Hakan kuma yana matukar yi mana dadi, domin babu abinda yafi a yi wa wani naka fatan alheri ko bayan ransa inji Hanafi.
Ya kuma kara da cewar kuma har yanzu mu da muke ‘ya’yansa mukan samu wata alfarma a sanadiyarsa, domin a wasu lokutan akwai wuraren da ban kai in shiga wajen ba.
Amma saboda kasancewata dansa sai a barni in shiga ba tare da wani shinge ko kyara ba.
Hakan yasa muke matukar godiya da yadda mutane ke saka shi a cikin addu’oinsu a kowane lokaci,kuna muna fatan Allah SWA ya kyautata makwancinsa.