‘Yan Nijeriya na kashe kimanin naira tirilyan 1.5 a kan gas din girki a duk shekara, wanda wannan adadin na iya zarcewa a shekara mai zuwa, saboda ci gaba da tashin gwauron zabin gas din girki ke yi.
Hakan dai ya tilasta wa miliyoyin ‘yan Nijeriya komawa amfani da gawayin wajen dafa abinci, wanda hakan ya janyo jefa fargaba a zukatan ‘yan kasar kan shirin yin amfani da makamashi da kuma yadda farashin kalanzir ke ci gaba da tashi.
- Abin Da Ya Sa Farashin Amfanin Gona Ke Ci Gaba Da Tashi A Nijeriya
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas:Â Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
Hukumar da ke lura da hako man fetur na kan tudu (NMDPRA) ta ce, a Nijeriya duk shekara na yin amfani da tan miliyan 1.4 na gas din girki.
Wannan ya kai yawan kilo biliyan 1.4, inda a yanzu farashin ya kai naira 1,100 kan kowanne kilo daya, yawan masu saye ke kashe naira tiriliyan 1.5 a duk shekara.
Samar da saukin da gwamnatin kasar ta yi kan harajin na BAT na naira 7.5, hakan ya nuna cewa, gwamnatin ta yi ragin da ya kai na kimanin Naira biliyan 10.5, na kudin shigar da ya kamata ta samu.
Bugu da kari, kalubalen da ake samu a fannin samun kudaden musaya na kasar waje tare da kuma tsadar man dizil, hakan ya janyo tarnaki a kan alfanun saukin da aka samar wa masu amfani da gas din girki a kasar nan.
A cewar hukumar kididdiga ta kasa (NBS), a 2018, ana kashe naira 2,084.74 don a zuba kilo biyar a na gas din girki din cikin silinda tare da kuma kashe naira 416 A 2018.
A 2019, farashin kilo daya ya ragu zuwa naira 334.08; inda kuma a 2020 farashin ya kai naira 389.4, sai kuma a 2021, farashin ya kai naira 353.76, wanda kuma farashin ya yi tashin gwauron zabi zuwa naira 843.6 a 2022.
 Watan Disabar 2023 kuwa, farashin kilo daya ya kai naira 1,100.