ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Farashin Amfanin Gona Ke Ci Gaba Da Tashi A Nijeriya

by Abubakar Abba
3 years ago
Gona

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Farashin kayan abinci a Nijeriya na ci gaba da tashin gwauron zabi; wanda za a iya cewa, ba a taba ganin irin hakan a shekaru da dama da suka wuce a wannan kasar ba.

Wannan matsalar na faruwa ce a yayin da wasu manona har yanzu ke kan yin girbin amfanin gonakinsu. Babu shakka, hakan na ci gaba da jefa fargaba a zukatan masu ruwa da tsaki a kan yadda matsalar za ta yi wa  fannin tattalin arzikin kasa illa tare da jawo rashin samar da  wadatacen abinci a wannan kasa.

  • Rikicin Siyasar Jihar Ribas:  Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
  • Kamfanin Man Nijeriya Ya Sa Hannu Kan Fasahar Gano Sinadarin Methane

Sai dai, ba Nijeriya ce kadai ke fuskantar irin wannan kalubale ba, musamman ganin cewa kasar ta mayar da hankali ne wajen shigo da amfanin gona daga kasashen ketare kamar abin da ya shafi Rogo da Doya da sauran kayan abinci.

Kazalika, Nijeriya na fuskantar karancin abinci kamar Masara, Alkama da Waken Soya. Har ila yau, faduwar darajar naira a kasar ya kara tabarbara al’amura wajen shigo da kayan abinci cikin kasar.

Abin Da Ya Sa Farashin Abinci ke Tashi:

Wani bincike da aka gudanar a wasu manyan kasuwannin kasar nan da ake yin hada-hadar sayar da hatsi ya nuna cewa, duk da manoma sun girbe amfani mai yawa a noman da aka yi na bana, amma farashin kayan abinici na ci gaba da tashin gwauran zabi.

Misali a Jihar Katsina, farashin na ci ngaba da tashi; inda lamarin ke ci gaba da tayar wa da magidanta hankali, musamman ganin cewa, ana fara shirin shiga sabuwar shekarar 2024 ta fara yin wani noman.

Wani dilan sayar da hatsi a Jihar Kano, Alhaji Sa’adu Abashe ya yi nuni da cewa, akasarin mutane ba su da masaniya a kan abin da ke jawo tashin farashin amfanin gonar da aka noma na bana.

Sannan, ya danganta tashin farashin a kan faduwar darajar naira da tsadar takin zamani da kayan aikin noma da kudaden da ake biyan ‘yan kwadago da tsadar farashin man fetur da kuma kudin da manoma ke kashe wa domin yin jigilar amfanin da suka noma daga gonakinsu zuwa kasuwanni don sayarwa.

Sa’adu ya kara da cewa, farashin Masara, Dawa, Waken Soya, Gero da kuma Shinkafa ya yi matukar karuwa, inda kowane buhu daya mai nauyin kilo 100 ya kai kimanin naira 30,000.

Shi kuwa wani babban dan kasuwa a kasuwar Dandume da ke a Jihar Katsina, Alhaji Muhammad Salisu ya sanar da cewa, gannin yadda a bara masu sayen hatsi suna boyewa, don sayar da shi da tsada sun samu makudan kudade, hakan ne ya sa wasu masu kudin su ma suka sayi amfanin gonar da dama da aka noma a bana; suka boye domin  samun kazamar riba.

Ya ce, wadanda suka sayi duk buhun Masara daya a kan naira 18,000 zuwa Naira 22,000, yanzu suna sayar da duk buhu guda kan akalla naira 55,000.

Shi kuwa Shugaban Kaungiyar Manoma Reshen Jihar Kano (AFAN), Malam Abdulrasheed Magaji Rimingado, ya danganta tashin farashin ne kan yadda wasu kamfanoni da ke sarrafa amfanin gonar zuwa wasu nau’ikan abinci ke yin rige-rigen saye amfanin da kuma tsadar jigilar amfanin gona.

A Jihar Neja kuwa, ‘yan kasuwa da manoma a jihar sun dangata tashin farashin a kan yadda ake yawan bukatar amfanin gonar. Shugaban masu sayar da hatsi a kasuwar sayar da hatsi ta Lemu a Karamar Hukumar Gbako, Alhaji Danladi Kowangi cewa ya yi; farashin buhun Shinkafar da ake nomawa a kasar nan ya tashi daga naira 22,000 zuwa naira 26,000, duk kuwa da cewa manoman sun jima da girbe Shinkafar.

Kowangi ya kara da cewa, sannan duk buhun Masara guda a halin yanzu, ana sayar da shi a kan naira 35,000, inda kuma ake sayar da buhun Gero a kan naira 35,000 a wannan kasuwa ta Lemu.

Har ila yau, a kasuwar Batati da ke Karamar Hukumar Labun a jihar da ake samun kayan abinci a cikin rahusa, ana sayar da duk buhun Dawa a kan naira 30,000, Gero naira 23,000, sai buhun jan Wake kuma a kan naira 40,000 zuwa naira 45,000.

A Karamar Hukumar Saminaka da ke Jihar Kaduna kuwa, shugaban masu sayar da hatsi a kasuwar, Manu Isah Idris ya danganta abubuwa da dama da suka jawo ci gaba da tashin farashin a daidai wannan lokaci; daga cikinsu a cewar tasa akwai batun yakin da ake ci gaba da yi a Kasashen Ukraine da kuma Kasar Falasdin tare kuma da cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayya ta yi.

Gona
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
An Fara Gina Cibiyar UHD Highland Ta CMG

An Fara Gina Cibiyar UHD Highland Ta CMG

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.