Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayar da takardar shaidar lashe zabe ga mambobin majalisar dokokin jihar Filato su 16 a ranar Asabar.
Mambobin sun kasance ne a mazaunin wadanda suka lashe zaben ranar 18 ga watan Maris bayan da kotun daukaka kara ta soke wadanda INEC ta bayyana a farko.
- INEC Ta Bada Umarnin Sake Zabe A Wasu Sassan Jihar Kogi
- Sada Zumunci Da Abubuwan Da Ke Yanke Shi A Zamanin Nan
Daga cikin mambobi 16 da aka baiwa takardar shaidar lashe zaben, 15 sun fito ne daga jam’iyyar APC mai mulki sai kuma daya daga jam’iyyar LP.
Dakta Oliver Agundu, Kwamishinan Zabe na Jihar Filato (REC), ya ce, bayar da sabuwar shaidar lashe zaben ya biyo bayan umarnin da kotun daukaka kara ne ta bayar.
Agundu ya bayyana cewa, kotun daukaka kara ta umurci hukumar INEC da ta baiwa wadannan ‘yan majalisar takardar shaidar lashe zabe a matsayin halastattun wadanda suka lashe zaben.
Agundu ya taya zababbun ‘yan majalisar murna bisa nasarar da suka samu tare da yi musu fatan alheri acikin tafiyarsu ta hidimar kasa.