Duniya mai ya yi, kungiyar Wolves ta diga wa Chelsea radadi, inda ta samu nasara da ci 2-1 a wasan farko na bikin Kirisimeti a gasar Firimiya tun 1995.
Duk da cewa, Kungiyar Chelsea da ke bakunci a filin wasa na Molineux ta taka leda sosai, sai dai ta yi bari da yawa inda ta gaza cin moriyar damarmakin da ta samu.
- Haaland Ya Zama Gwarzon Dan Wasan Duniya Na BBC A Bana
- MDD Ta Sanar Da Bikin Bazara Na Sin A Matsayin Daya Daga Bukukuwan Da Za A Rika Kiyaye Kimarsu
Mario Lemina da Matt Doherty ne suka zura wa Chelsea kwallo a raga daga bisani kuma dan wasa Christopher Nkunku, ya farke kwallo daya inda aka tashi da ci 2:1.
Talla
Wannan rashin nasara ya haifar da rashin daidaituwa ga Chelsea, wanda yasa ta makale a matsayi na 10, yayin da Wolves ke biye da ita a matsayi na 11.
Talla