Rundunar sojin Nijeriya ta ce an kashe mutane sama da 100 a wani farmaki da gungun mahara suka kai a kauyen Mushu da ke Jihar Filato.
Mai magana da yawun rundunar sojin ‘Operation Safe Heaven’ a Jihar Filato, Kaftin Oya James, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an kai hari kan kauyen Mushu da tsakar daren ranar Asabar.
- Gwamnatin Sakkwato da Wamakko Sun Tallafa Wa Mutane 66 Da Sojoji Suka Ceto
- Zaben Cike Gurbi: APC Za Ta Sayar Da Takardar Tsayawa Takarar Sanata Naira Miliyan 20
Wani mazaunin kauyen kuma mai suna Markus Amorudu, ya ce gungun ‘yan bindigar sun yi musu bazata kasancewar sun afka musu ne yayin da suke tsaka da barci, inda da duk da cewar da dama daga cikinsu sun boye, sai da aka yi awon gaba da wasu, baya ga wadanda suka jikkata.
Har yanzu dai ba a gano dalilin kai farmakin ba, zalika ba a kuma tantance ‘yan ta’addan da suka kai harin ba.
Sai dai tuni aka aike da tarin jami’an tsaro zuwa kauyen na Mushu da ke karamar hukumar Bokkos, domin tabatar da tsaro.
Al’ummar Jihar Filato dai sun shafe shekaru da dama suna fama da tashe-tashen hankula da suka hada da rikicin kabilanci, addini da kuma hare-haren ‘yan bindiga.