Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta yi barazanar dakatar da kungiyar kwallon kafa ta kasa da kungiyoyin kwallon kafa na kasar Brazil daga buga gasar kasa da kasa, idan har hukumar kwallon kafa ta kasar ta shiga tsakani wajen zaben sabon shugaban hukumar a watan Janairu.
FIFA ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ta aike wa wani jami’in hukumar kwallon kafa ta Brazil (CBF) inda ta ce, hukumar na iya fuskantar dakatarwa idan ba ta yi biyayya ga kiran FIFA na jira ba, saboda hukumar na shirin bijerewa ta gudanar da zaben cikin gaggawa don maye gurbin Ednaldo Rodrigues a matsayin shugaban hukumar.
- Kwallon Mata: FIFA Ta Sauya Filin Wasan Da Za A Buga Wasan Nijeriya Da Burundi
- Tsarabar Kirsimeti: Yadda Wolves Ta Zazzaga Wa Chelsea Ci A Gasar Firimiya
A cewar rahotannin ESPN da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press, Kotun Rio de Janeiro ta kori Rodrigues da dukkan wadanda ya nada a hukumar CBF daga mukaminsu a ranar 7 ga watan Disamba saboda wasu kura-kurai da aka samu a zabensa na bara. Manyan kotunan Brazil biyu sun amince da hukuncin a makon jiya.
Hukuncin da aka yanke wa Rodrigues mai shekaru 69 na iya yin illa ga yunkurin Brazil na karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata a 2027 da kuma yunkurin da yake yi na daukar kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya jagoranci tawagar kasar a shekara mai zuwa.