Tsohon kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba, ya rasu.Â
Na’Abba, wanda ya taba zama kakakin majalisar wakilai ya rasu da sanyin safiyar ranar Laraba.
- Mutane 96 ‘Yan Bindiga Suka Hallaka A Filato – ‘Yansanda
- Sin Ta yi Nasarar Harba Tare Da Gwada Taurarin Dan Adam Na C Karo Na 24
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken rahoto game da rasuwarsa.
An zabe shi dan majalisar wakilai a shekarar 1999 daga Jihar Kano.
Ya zama shugaban majalisar ne ‘yan watanni bayan kaddamar da majalisar biyo bayan murabus din shugaban majalisar na wancan lokaci, Salisu Buhari daga Jihar Kano, kan badakalar jabun takardun makaranta.
Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:30 na rana, a Kofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano.