Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba.
A wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Mista Edwin Olofu ya fitar, Ganduje ya bayyana Na’Abba a matsayin cikakken dan siyasa kuma dan majalisa wanda ke nufin alheri ga kasa.
- Da Sannu Za Mu Farfado Da Manchester United – Jim Ractliffe
- Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba Ya Rasu
Ganduje ya bayyana irin gagarumar rawar da Na’Abba ya taka a lokacin da ya rike mukamin Kakakin Majalisar Wakilai na tabbatar da ‘yancin kai na bangaren gwamnati.
Ya kara da cewa, “Ayyukan da ya yi sun taimaka ga duk wani nasarorin da muka samu a majalisar dokokin kasar nan a yau.
“Ya yi wa Nijeriya hidima da himma, hazakarsa, kwazonsa da mutuntakarsa don ciyar da mu gaba,” in ji shi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya sanya shi a Aljanna Firdausi, ya kuma bai wa daukacin iyalansa da al’ummar Jihar Kano da ma Nijeriya baki daya hakurin rashin sa.