Gwamnatin tarayya ta sha alwashin zakulo wadanda suka halaka mutane fiye da 160 a ranar Lahadi a Jihar Filato.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne, ya bayyana hakan a wata ziyarar jaje, ga wadanda suka hadu da ibtila’in hare-haren ‘yan bindiga a garin Bokkos, da ke Jihar Filato.
- Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Kasuwannin Shanu 11 Saboda Matsalar ‘Yan Bindiga A Jihar
- Bikin Kirsimeti: Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Hare-haren Filato
Shettima ya bayyana takaicinsa kan kisan mutane fiye da 160, da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.
Ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don taimaka wa wadanda lamarin ya shafa.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang wanda shi ma ya nanata yunkurin gwamnatinsa na tabbatar da cewa wadanda suka aikata mugun aikin sun fuskanci hukunci.
Ya kuma ce zuwan mataimakin shugaban kasa ya nuna cewa gwamnati na da niyyar taimakawa.
Hakimin Gundumar, Mbar a Karamar Hukumar Bokkos, Danjuma Rafan ya ce harin ya ba su mamaki saboda babu wani abin da ya hada su da abokan zamansu.
Shi kuma shugaban kungiyar Fulani ta Gan Allah a Karamar Hukumar Bokkos, Saleh Yusuf Adam ya ce su ma a bangarensu an sa ce musu dabbobi an kuma kashe musu mutane.
Tun farko shugaban Karamar Hukumar Bokkos, Monday Kassa ya ba da adadin mutane 148 ne aka kashe a kauyuka 25.
Gidaje 1290 aka kone kurmus a cewar shugaban.
Maharan sun kuma kone motoci 81, babura 187, injinan ban ruwa 267, yayin da mutane 87 da suka samu raunuka.