Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi nasarar tarwatsa wasu gungun masu aikata laifuka da suka kware wajen safarar kananan yara, wadanda suka shafe shekaru da dama suna gudanar da muggan ayyukansu a jihar.
Bayan gano asirinsu, rundunar ‘yansandan ta cafke ‘yan kungiyar da dama, wadanda suka kasance suna gudanar da ayyukansu a jihohin Kano, Bauchi, Anambra, da Imo.
- Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓen Kano, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kasafin Biliyan 437.3 Na 2024
Da yake magana a wani taron manema labarai a Kano a ranar Alhamis, kwamishinan ‘yansandan jihar, Muhammad Usain Gumel, ya ce binciken farko da aka gudanar ya kai ga cafke wadanda suke aikata wannan muggan laifukan tare da kwato wadanda suka sace.
Ya ce, a ranar 15 ga Disamba, 2023, wata mata mai suna Comfort Amos, mai shekaru 45, an kama ta a tashar babbar mota ta Mariri da ke Kano a lokacin da take kokarin tafiya da Abdulmutallib Sa’ad mai shekaru biyar zuwa jihar Legas. Binciken da aka gudanar ya kai ga cafke wasu da dama da suka hada da Chika Ezugbu, Joy Nzelu, Clement Ali, da Emeka Ekeidigwe, wadanda dukkansu mazauna Kano ne da ke cikin kungiyar ta safarar kananan yara.
An gano cewa, an sace Sa’ad mai shekaru biyar ne a ranar 12 ga Disamba, 2023, daga Zango kwatas a jihar Bauchi.
Bugu da kari, Kwamishinan ya bayyana cewa, an kama wasu ‘yan kungiyar guda biyu Ruth Yerima da Abner Samuel a Bauchi, yayin da wani mai suna Ndemma Obi kuma aka kama shi a Legas sai kuma Ebere Eriobuna a jihar Anambra.