Hukumar lura da harkokin kasuwanci ta kasar Sin ko SAMR a takaice, ta ce adadin masu yin rajistar sabbin sana’o’i a kasar ya karu cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, wanda hakan ke nuna cewa, manufofin Sin masu ruwa da tsaki suna taka rawa, kana yanayin kasuwanci na samun kara kyautatuwa a kasar.
Alkaluman SAMR sun nuna cewa, a tsakanin watannin 11, an yi rajistar sabbin sana’o’i sama da miliyan 30.2, adadin da ya karu da kaso 10.5 bisa dari bisa na makamancin lokacin shekarar bara. Kaza lika sabbin kamfanoni da aka yi wa rajista sun karu da kaso 14.6 bisa dari, yayin da sana’o’in dogaro da kai da aka yi wa rajista suka karu da kaso 8.9 bisa dari.
A bana, an samu ci gaban sana’o’i da kamfanoni bisa daidaito, wanda hakan ke nuni ga karin inganci, da fadadar karkon kasuwannin kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp