A ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2023, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun tura wa juna sakwanni don murnar sabuwar shekarar 2024 da ke tafe.
Xi ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2023, su biyu sun gana da juna fuska da fuska har sau biyu a Moscow da Beijing, inda suka yi musayar ra’ayoyinsu kan dangantakar dake tsakaninsu da manyan batutuwan duniya da ke jawon hankalinsu, kuma sun cimma ra’ayi daya. Jimillar cinikayya a tsakanin Sin da Rasha ta kai dalar Amurka biliyan 200 kafin lokacin da aka tsara. Xi ya ce, a sabuwar shekara mai zuwa, yana son ci gaba da mu’amala tare da Putin, da kuma yi amfani da damar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, wajen jagorantar kasashen biyu don kara amincewar juna, da inganta hadin kansu, da kyautata zumunta, a kokarin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha yadda ya kamata.
A nasa bangaren, Putin ya bayyana cewa, yana da imanin cewa, bisa kokarin kasashen biyu, za su kara samun kyawawan sakamako bisa hadin kansu a fannoni daban daban. Kana za su samu sabon ci gaba ta fuskar hadin gwiwa a karkashin inuwar tsare-tsaren MDD, G20, Kungiyar hadin kan Shanghai, da kuma BRICS.(Kande Gao)